Liman Farms

Liman Farms Research| Consultant| Farmer| Business

KUSKUREN DA KE LALATA ALLURAR KAJI.Manoma da yawa suna sayen Lasota da Gumboro amma ba su san cewa zafi yana lalata allu...
24/03/2026

KUSKUREN DA KE LALATA ALLURAR KAJI.

Manoma da yawa suna sayen Lasota da Gumboro amma ba su san cewa zafi yana lalata allurar ba.

Idan aka dauko allurar kaji ba tare da kankara ko ice pack ba, cikin kankanin lokaci ingancinta zai ragu.

Lokacin da za ta iya zama ba tare da kankara ba

• Idan yanayi ba zafi sosai ba awa 1–2 kacal yake iya zama.
• Idan zafi ya yi yawa (kamar lokacin rana) awa 1 ko kasa da haka

Idan ta wuce wannan lokaci:
Ingancin allurar zai ragu.
Rigakafin ba zai yi aiki sosai ba.
Kaji za su iya kamuwa da cuta.

A rika daukar allura cikin kankara
A ajiye ta a fridge tsakanin 2–8°C
A yi amfani da ita nan da nan bayan an bude

Rashin kiyaye wannan shiyasa kaji suke kamuwa da cututtuka.

Kafin ka fara kiwon kajin hausa ka fara karanta wannan rubutun daga farko.1. Ka tabbatar da ka samo kajin kiwo masu kyau...
19/03/2026

Kafin ka fara kiwon kajin hausa ka fara karanta wannan rubutun daga farko.

1. Ka tabbatar da ka samo kajin kiwo masu kyau da lafiya.

2️. Dole ne ka samar da daki mai kyau sannan ka tabbatar kana da karamin filin da zasu dinga zagayawa.

3. Dole ya kasance kai kake hada musu abincin da kake basu

4️. Dolene ka rike yin rigakafi akan lokaci.

5. Dolen e ka samar masu da gurin yin kwai isasshe wanda baza su na dinga hade kwai ba.

6️. Dolene ka nemi littafi kana rubuta bayanan kiwon.

Idan har ka rike waɗannan zaka yi nasara In sha Allah.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING

DOMIN GINA GIDAN GONA CIKIN SAUƘI.Ka samu ƙaton zakaranka na Maja (Noiler) guda ɗaya da kajin Hausa matasa wanda suke da...
18/03/2026

DOMIN GINA GIDAN GONA CIKIN SAUƘI.

Ka samu ƙaton zakaranka na Maja (Noiler) guda ɗaya da kajin Hausa matasa wanda suke daf da fara kwai guda goma ka dan samu waje ka killacesu kaga ikon Allah.

A kalla su samu kiwo na wata ɗaya, kuma karka damu kanka wajen basu dusar kamfani, ka basu ta hausa ko kuma idan akwai babban waje ka barsu suyi kiwonsu a tsakar gida, tare da kulawa.

Indai wanda suke daf da fara kwai ka saya ka musu kiwon wata daya kowacce zata iya fara kwai kuma ta kyankyashema kayanka.

Mu sa kowacce zata kyankyashe ma guda bakwai kawai a kalla a wata biyu da sayensu da kyankyasa.

A kalla fa kana targeting 'ya'ya saba'in kuma indai zakaran maja (Noiler) ne to yaran masu saurin girma ne insha Allah.

Idan sunyi sati daya a wajen iyayen zaka iya daukesu kayi brooding dinsu da kanka, kana raba iyayen da yaran su zasu sake maka kwai a kalla a shekara zaka iyayin wannan sau hudu da izinin Allah.

A shekarar farko kana targeting 'ya'ya 280 kuma su 'ya'yan duk Wanda yayi akalla wata hudu zuwa 5 suma zasu fara nasu kwan da izinin Allah.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

TATTABARUNA SUNYI KWAI HUƊU.Wani yace Adam ina cikin alkhairi tattabaru na siya tun suna yara ('yan shila) sun girma har...
17/03/2026

TATTABARUNA SUNYI KWAI HUƊU.

Wani yace Adam ina cikin alkhairi tattabaru na siya tun suna yara ('yan shila) sun girma har sunyi kwai huɗu kuma sun kwanta kwanci. Dama ana samun haka tattabara tayi kwai har guda huɗu?

Nace mai eh mana ana samu amma fa akwai matsala, yace matsalar kuma? Nace kwarai kuwa, bari ka ji inda matsalar take.

Idan ka ga tattabarunka sunyi kwai biyu to ka rabasu ka yiwa ko wacce aure domin "Auren Jinsi" suke, normal zaka ga suna yin barbara kamar mace da namiji amma kwan ba zai taɓa fita ba saboda ba namiji (infertile) ne.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING

DOMIN INGANTA SANA'ARKA TA KIWO.Idan kana son inganta harkarka ta kiwo, dole ne ka fahimci cewa kiwo ba kawai saka dabbo...
16/03/2026

DOMIN INGANTA SANA'ARKA TA KIWO.

Idan kana son inganta harkarka ta kiwo, dole ne ka fahimci cewa kiwo ba kawai saka dabbobi a gona ba ne. Kiwo sana’a ce da take bukatar tsari, hakuri, da bin ka’idoji. Duk wanda yake son ganin gonarsa ta yi kyau tare da samun nasara, dole ya dauki lokaci yana kula da dukkan abubuwan da s**a shafi kiwo.

Abin da ake yawan gani shi ne, wasu manoma suna yawan korafi da matsaloli a gonarsu. Wani zai ce kajinsa suna mutuwa, wani zai ce basa yin kwai, wani kuma zai ce yana kashe kudi amma baya ganin riba. Amma idan ka bincika sosai, za ka ga cewa mafi yawancin matsalolin suna faruwa ne saboda rashin kulawa da bin ka’idojin kiwo.

Misali, wasu basa kula da tsabtace gidan gona, alhali datti yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo cututtuka. Wasu kuma basa bin jadawalin allurai (vaccination) yadda ya kamata, wanda hakan kan sa kaji su kamu da cuta cikin sauki. Haka kuma akwai wadanda basa kula da ingancin abinci da ruwa, alhali wadannan abubuwa sune ginshikin wajen samar da lafiyar dabbobi.

Wani babban kuskure kuma shi ne rashin lura da alamar matsala da wuri. Idan manomi ya ga dabbarsa tana nuna wata alama ta rashin lafiya amma ya yi shiru, to yana iya jawo babbar asara a gaba. Amma idan aka lura da matsalar da wuri, sau da yawa ana iya shawo kanta kafin ta zama babbar matsala.

Saboda haka yana da kyau duk manomi ya rika tsayawa yana duba gonarsa da kyau.

Ka tambayi kanka:
Shin ina kula da tsafta yadda ya kamata?
Shin ina ba dabbobina ingantaccen abinci?
Shin ina bin jadawalin allurai?
Shin ina lura da duk wata alama ta matsala da wuri?

Idan ka rika yin wannan bincike a kai a kai, za ka ga cewa matsaloli suna raguwa sosai, kuma gonarka zata fara kawo maka riba kamar yadda kake so.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

MUTANE BA ZA SU YARDA DA KAI BA.Lokacin da ka fara gina gidan kaji.Lokacin da kake sayen ƙananan kaji (chicks)Lokacin da...
16/03/2026

MUTANE BA ZA SU YARDA DA KAI BA.

Lokacin da ka fara gina gidan kaji.
Lokacin da kake sayen ƙananan kaji (chicks)
Lokacin da kake fama da ƙalubale.

Amma za su yarda da kai:

Lokacin da s**a ga motar ɗaukar kwai a gidan gonarka
Lokacin da s**a ga ka buɗe babban gidan gona
Lokacin da s**a ga ka ɗauki ma’aikata.

Ga duk wanda yake son shiga harkar kiwo:

Ka nemi ilimi.
Karka tsaya saboda maganar mutane.
Ka fara da kaɗan.
Ka koyi rigakafi da kulawa.
Ka yi haƙuri da juriya.
Karka yanke ƙauna.

A harkar kiwo nasara ba ta zuwa da sauri, amma tana zuwa ga wanda bai daina ba.

Allah yasa mu dace.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

Ka gwada zuba tattabaru Aure goma (10) ka samar musu da yanayi mai kyau tare da kulawa, ruwa da abinci mai inganci. Ka b...
15/03/2026

Ka gwada zuba tattabaru Aure goma (10) ka samar musu da yanayi mai kyau tare da kulawa, ruwa da abinci mai inganci. Ka basu shekara daya za ka sha mamakin irin tattabarun da za ka samu cikin shekara daya.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

Tattabara uwar alƙawari komai dare gida za ta kwana.Idan ta birgeka ka danna alamar ❤️     LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK F...
15/03/2026

Tattabara uwar alƙawari komai dare gida za ta kwana.

Idan ta birgeka ka danna alamar ❤️



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

Idan so samu ne daga lokacin da talotalonka ta fara kwai kawai ka rabata da namijin. Yin hakan zai rage maka asarar kwai...
15/03/2026

Idan so samu ne daga lokacin da talotalonka ta fara kwai kawai ka rabata da namijin. Yin hakan zai rage maka asarar kwai sosai. Saboda a harkar kiwon talotalo Barbara ita ce kawai amfanin namijin. Idan kuwa ya yi har ta fara kwai amfaninsa Kuma ya kare sai bayan ta gama kwai.

Shi namijin talotalo ya na iya fasa kwai. Ya na iya kashe 'ya'yanma. Ni shaida ne akan haka!

Shi yasa na ce ba a barin Namijin talotalo kusa da kwai ko Kuma kusa da jarirai. Illatasu zai yi.

Idan talotalon ta fara kwai ko dai ka killaceshi ka dinga bashi abinci ya na ci ko kuma ka kara mishi Aure.



LIMAN POULTRY AND LIVESTOCK FARMING ✍️

Idan zafi ya tsananta har wanka anayi musu, amma banda kansu.
14/03/2026

Idan zafi ya tsananta har wanka anayi musu, amma banda kansu.

Address

Sharada Phase III, Ja'en Ado Bayero Juma'at Mosque, Behind Big Trust Academy
Kano

Telephone

+2347040409589

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Liman Farms posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Liman Farms:

Share