16/07/2026
Janar Yahya Rahim Safavi ya ce:
🚫 Kai hari da makamin nukiliya kan Iran zai zama ɗaya daga cikin matakan da ba su da hikima ko kaɗan. Kuma mafi kuskure a tarihin Duniya
🚫 Iran Ba Karamar kasa nace kawai, Faɗin ƙasar Iran ya kai kusan kilomita murabba'i miliyan 1.6. Wani babban ɓangare na ƙasar hamada ce, kuma ko da harin nukiliya na ƙaramin ƙarfi (tactical nuclear strike) zai haddasa mummunar asara da salwantar rayuka masu yawa, ba zai iya hallaka Iran gaba ɗaya ba.
🚫 Duk da irin wannan hari, girman ƙasar Iran zai ba ta damar ci gaba da wanzuwa.
🚫 Sai dai, a martani da yayi, ya bayyana cewa, za mu kai hare-hare kai tsaye kan cibiyar nukiliya ta Dimona da sauran cibiyoyin nukiliyar Isra'ila. Ga ƙasa ƙarama kamar Isra'ila, hakan zai haifar da mummunar barna fiye da wadda za ta samu Iran. Zaɓin yana hannun Amurka.